Acts 26

1Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.” Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa. 2Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi saʼa da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa, 3musamman ma domin ka saba sosai da dukan alʼadun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.

4“Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima. 5Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne. 6Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shariʼa yau. 7Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena. 8Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana ta da matattu?

9“Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare. 10Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, saʼad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuriʼata gāba da su. 11Sau da dama nakan bi majamiʼa-majamiʼa, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.

12“A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci. 13Da tsakar rana, Ya sarki, saʼad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata. 14Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Aramayik, ‘Shawul, Shawul, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokana dabba.’

15“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’

“Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.’
16‘Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Alʼummai. Ina aikanka zuwa gare su domin 18ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

19“Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba. 20Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, saʼan nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Alʼummai su ma, na yi waʼazi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu. 21Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni. 22Amma na sami taimakon Allah har yǎ zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru—  23cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Alʼummai.”

24A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”

25Bulus ya amsa, ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau. 26Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba. 27Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.”

28Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?”

29Bulus ya amsa, ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa-ina adduʼa ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”

30Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su. 31Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko ɗauri.”

32Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.”

Copyright information for HauSRK